Ƴan bindiga a Zamfara sun buƙaci kuɗin fansan wasu mutane da sabon Naira.

Ƴan bindiga a Zamfara sun buƙaci kuɗin fansan wasu mutane da sabon Naira.

Bayan Garkuwa Dawasu Mutane ‘Yan Bindiga Sun Buƙaci Kuɗin Fansa Da Sabon Naira.

 

Wasu ‘yan ta’adda da suka yi garkuwa da mutane huɗu da suka hada da namiji da mace da yara biyu a ƙauyen Kolo da ke ƙaramar hukumar Gusau a jihar Zamfara.

 

 

An tattaro cewa bayan sace waɗanda aka yi garkuwa da su, ‘yan bindigar sun buƙaci a biya su Naira Miliyan (Goma) N10m, kuma tare da gindaya sharaɗin rashin amincewa da tsoffin takardun naira.

 

 

 

Wani ɗan asalin yankin mai suna Mohammed Ibrahim, ya ce daga baya ‘yan fashin sun rage kuɗin fansa zuwa Naira Miliyan (Biyar) N5m, inda ya ce mutanen ƙauyen sun yi ta ƙoƙarin tara kuɗin fansar domin a sako waɗanda lamarin ya shafa.

 

“A yayin da muke ƙoƙarin tattara kuɗaɗen da ‘yan ta’addan suka nema, sun sake aike da wani saƙon a safiyar yau cewa ba za su karɓi tsoffin takardun naira ba.

 

“Sun ce za su cigaba da ajiye mutanen da aka sace a sansanonin su har sai an fitar da sabbin takardun Naira a watan Disamba,” in ji Ibrahim.

 

Kiraye-kirayen da aka yi wa jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, da kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Ibrahim Dosara, ya ci tura.

 

Har yanzu ba a amsa saƙonnin rubutu da aka aika zuwa lambobin wayarsu ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

 

A wani labarin kuma a ranar Talata, wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani dan siyasar jam’iyyar All Progressives Grand Alliance, Nduka Anyanwu, a jihar Imo.

 

An tattaro cewa, Anyanwu, wanda daya ne daga cikin ‘yan takarar majalisar wakilai na jam’iyyar, yana yakin neman zaɓe tare da magoya bayansa a lokacin da ‘yan bindigar suka mamaye taron tare da fatattake shi.

 

Da take ba da labarin yadda aka yi garkuwa da shi, wata majiya ta ce, “’yan bindigar sun tare shi (Anyanwu) a hanya a lokacin da zai kammala shirye-shiryen gudanar da zaben wakilan sa. Har yanzu ba mu san inda suka kai shi ba kuma har yanzu masu garkuwa da mutanen ba su yi wata magana ba.”

 

Da aka tuntubi shugaban jam’iyyar APGA a jihar, John Iwuala, wanda ya tabbatar da sace dan siyasar ya ce an sako dan siyasar.

 

Iwuala ya ce, “Eh, an yi garkuwa da dan takararmu da sanyin safiyar yau, amma a lokacin da muke shirin bayar da rahoto a hukumance, sai muka ji cewa masu garkuwa da mutane sun sako shi. Masu garkuwa da mutanen sun tattara duk abin da yake tare da shi kamar lokacin da aka yi garkuwa da shi.”

 

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Mike Abattam, ya ce har yanzu ba a sanar da shi lamarin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button