Wata Koto A Garin Abuja Ta Soke Nasar Da Gawuna Yayi A Koto Kuma Ta Bayyana Dalili Wato Audu Bulama Bukarti ya wuce tunanin yaro indai a fa...
Wata Koto A Garin Abuja Ta Soke Nasar Da Gawuna Yayi A Koto Kuma Ta Bayyana Dalili
Wato Audu Bulama Bukarti ya wuce tunanin yaro indai a fannin shari'a ne
ga kuma ilimin addinin da son gaskiya da kuma taimakon mabukaci
Idan ka kalli fashin bakin da akayi a jiya a kan hukuncin shari'ar kano zaka tabbarda cewa waye bulama
Haka a kwanan baya suka gwabza da wani wanda ake cewa ”DAN JAHANNAMA ” Yayi masa mugun kaye da kwararan hujjoji
Sir muna maka fatan Alkhairi Allah ya tsareka da tsarinsa Allah ya kara shiga cikin lamuranka Allah ya kara kiyaye ka da tarkon makiya
Allah yasa a gama da duniya lafiya
Fashin Baƙi dangane da hukuncin da Tribunal tayi kan zaɓen gwamnan jihar Kano.
Daga Barrister Audu Bulama Bukarti .
Jiya da daddare lauyoyin jam'iyar NNPP da APC sun kwashe awanni suna fashin baki akan hukuncin kotun.
Barister Bashir lauyan NNPP ya kawo hujjojiin sa Kámar yadda dokar kasa ta tana da.
Shima na APC Barister Abdulrazaq yayi nasa baje kolin hujjojiin.
Daga karshe Barister Bulama Bukarti yayi dauraya, inda ya zaiyana inda kotun tayi daidai da akasin haka.
Bukarti yace bai kamata kotun ta soke kuri'un NNPP tabar na APC ba.
Ya kara da cewa kotun tayi kuskure wajen aiyana sunan Gawuna acikin takardar hukuncin data fitar.
Bulaman ya Kara da cewa a iya fahintar sa, wannan hukuncin hira ce irin na tebirin mai shayi.
Lauyoyin APC da NNPP duk sunyi matukar kokari wajen baiyana hujjojin su.
A gaskiyar magana Barister Abdulrazaq na APC yafi Barister Bashir na NNPP iya tsara bayani.
Barister Bashir na NNPP ya zaiyana hujjoji masu kyau, amma yadda zai tsara hujjojin ne a magana bayi dasu, ita kuma kotu da hujjoji take amfani.
Daga karshe Bulama yayi concluding da cewa abu biyu ne yake da yakinin zai faru,
1) kọ a tafi inconclusive a wa'incan akwatuna.
2) ko a soke zaɓen Baki ɗaya.
3) Ko abi dokar ƙasa da tace a Polling Unit kawai za'a iya soke zaɓe, wato collation officer ne kawai keda hurumin soke wa ba kotu ba.
Zamu cigaba da bibiyar shari'ar, da sauraran fashin baki daga bakin masana shari'a.
COMMENTS