Anyi Sallar Jana’izar Wasu Dattawa Mutum Uku Da Suka Rasu Lokaci Guda A Jihar Neja

Anyi Sallar Jana’izar Wasu Dattawa Mutum Uku Da Suka Rasu Lokaci Guda A Jihar Neja – Janzakitv

Yadda Al’ummar garin suleja dake jihar neja suka wayi gari da rasuwar wasu manyan dattajai lokaci daya batare da rashin lafiya ba tare dasu.

 

Sunayen Manyan dattajai da suka rasu a garin na suleja sune kamar haka: Alhaji aliyu abubakar shugaban kungiyar izala ta reshen garin suleja dake jihar naija.

 

Da kuma marigayi alhaji abubakar (Nagya) tare da marigayi alhaji Ibrahim baba (aljannu) mataimakin shugaban kungiyar izala ta garin suleja.

 

Hakika wadannan dattijai sun kasance mutane masu daraja a cikin garin na suleja haka zalika dattijan sun samu shaidu na musamman dangane da al’ummar garin.

 

Yanzu haka anyi musu sallar jana’iza lokaci guda kamar yadda addinin musulunci ya tanadar ayiwa dukkan musulmin daya rasu saidai muce ubangiji allah yayi musu gafara baki daya.

 

Mu kuma da muka rage idan tamu mutuwar tazo allah yasa mu mutu cikin masu imani tare da cikawa da kalmar shahada a bakin mu.

 

Kuci gaba da kasancewa da shafin gidan jaridar mu domin samun sabbin labaran mu kowace rana da kowani lokaci mungode

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button