BIDIYO: Mota Cike Da Miliyoyin Kudi Ta Kone Kurmus A Jihar Kebbi

BIDIYO: Mota Cike Da Miliyoyin Kudi Ta Kone Kurmus A Jihar Kebbi
Wata mota wadda ta dakko kudade masu tarin yawa ta kone kurmus a lokacin da take tafiya.
Wannan lamari dai ya faru ne a jihar Kebbi dake arewacin Najeriya kuma a ranar Laraba abin ya faru.
Bayan faruwar abin tuni ‘yan sanda su ka yi dirar mikiya a wajen domin ganin halin da ake ciki.
Sai dai wata majiya ta tabbatar da cewa kudina sun kone kurmus babu wanda za’a mora daga cikinsu.