Dan Fitaccen Mawakin Kudancin Najeriya Davido Ya Rasu

Dan Fitaccen Mawakin Kudancin Najeriya Davido Ya Rasu

Daga BBC

Rundunar ƴan sanda a jihar Legas da ke Najeriya ta ce ta gayyaci mutane takwas masu hidima a gidan shahararren mawaƙin nan Davido, domin gudanar da bincike game da rasuwar ɗan mawaƙin, mai shekara uku.

 

Mai magana da yawun rundunar, Benjamin Hundeyin ya tabbatar wa BBC cewar yanzu haka an ajiye gawar yaron a ɗakin adana gawa.

 

Hundeyin ya ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin da daddare, kuma ɗaya daga cikin ma’aikatan gidan ne ya kai rahoton lamarin a ofishin ƴan sanda.

 

Kakakin ƴan sandan ya kuma ce sun tattauna da iyayen yaron, yayin da suke ci gaba da bincike.

Ya ƙara da cewa za su saki duk wanda aka tabbatar ba shi da hannu a lamarin.

 

Kakanin ƴan sandan reshen jihar Legas ya ce “Abin da muka sani zuwa yanzu shi ne ya nutse ne a ruwa. Babu wani ƙarin bayani da muke da shi bayan wannan. Muna duba hotunan kyamarar tsaro ta gidan domin samun ƙarin bayani kan abin da ya faru.”

 

Har yanzu Davido da iyalansa ba su ce komai ba a kan mutuwar.

 

Tun da asubahin ranar Talata ne rahotanni ke cewa yaron mai suna Efeanyi ya rasu bayan ya faɗa wurin ninƙaya da ke cikin gidan.

 

Ifeanyi shi ne yaro ɗaya tilo da David Adeleke (Davido) ya haifa tare da budurwarsa Chioma Rowland.

 

A kwanakin baya ne dai Davido ya sanar da cewar zai auri mahaifiyar ɗan nasa (Chioma Rowland) a shekara mai zuwa (2023).

 

Sai dai gabanin mutuwar Ifeanyi, Davido yana da yara huɗu, waɗanda ya haifa da mata daban-daban.

 

Wannan lamari na zuwa ne bayan cikar yaron shekara uku da haihuwa a watan Oktoba.

 

Kwanakin baya wani bidiyo ya nuna yadda Davido ke koya wa ɗan nasa yadda ake yin iyo a wurin ninƙaya.

 

A shekarar 2018 ma, wani mawakin Najeriya mai suna Dbanj ya taɓa rasa ɗansa kwatankwacin haka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button