Google ya turawa wani mutum miliyan 150 bisa kuskure kuma yaki tuntubarsa

Google ya turawa wani mutum miliyan 150 ($250k) bisa kuskure, Wani mutum ya tashi kwatsam ya tsinci sakon kudi a account dinsa wanda bashi akayi niyyar turowa ba, Kamfanin Google shine ya tura kudin kuma yaki ya tuntubeshi domin yadawo da kudin. mutumin mai suna Sam Curry ya bayyana yadda abin yafaru a shafinsa na Twitter
Google ya turawa wani mutum miliyan 150 bisa kuskure
Sam Curry dai ma’aikacine na Injiniya a wani kamfani Yuga Labs, ya rubuta yadda sakon kudi ya sameshi daga Google a bisa kuskure
“Yanzu sama da sati 3 kenan tunda Google ya tura min $249,999 kuma har yanzu banji wani batu ba daga garesu, akwai wata hanya dazan iya tuntubar Google? ba komai idan basa so na dawo dashi.” Sam Curry ya rubuta a shafinsa na Twitter
It's been a little over 3 weeks since Google randomly sent me $249,999 and I still haven't heard anything on the support ticket. Is there any way we could get in touch @Google?
— Sam Curry (@samwcyo) September 14, 2022
(it's OK if you don't want it back…) pic.twitter.com/t6f7v5erli
Mutane da dama masu bibiyar Sam Curry a shafin Twitter sun bashi shawara gwargwadon abinda suka sani akan wannan lamari
Sai dai a wani rapoto da CNN ta wallafa ya bayyana yadda kamfanin Google ya tabbatar da tura kudin bisa kuskure kuma suna kan hanyar gyara abinda yafaru
Tsawon sati uku kenan wannan mutum bai kashe ko sisi ba daga kudin da aka tura masa, Amma idan kaine ya zakayi?
Karanta Wasu Karin Labarai: