Har Na Bar Duniya Bazan Kara kula wata mace ba, kuma ba zan taba Yin Aure Ba – Cewar Wani Saurayi Da Budurwa Ta Yaudara

Har Na Bar Duniya Bazan Kara kula wata mace ba, kuma ba zan taba Yin Aure Ba – Cewar Wani Saurayi Da Budurwa Ta Yaudara

Wani matashin saurayi ya bayyana cewa shi da yin aure har abada, har ya mutu ya koma ga Allah ba zai taba yin aure ba domin abinda budurwar sa ta yi masa.

 

 

 

Matashin mai suna Seyi Oluleye a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter yace yayi mamakin irin cin amanar da budurwarsa da zai aura tai masa.

 

 

 

Matashin yace ya gano cewa budurwar sa da suke shirin yin aure ta ci amanar sa inda ya kamata da wani namijin suna yin lalata, inda ya bayyana hakan da tsantsar cin amana.

 

 

Don haka nike bayyanawa duniya cewa nida ita babu batun aure kuma babu wata mace da zan kuma nema a matsayin matar aure, ni da yin aure har abada.

 

 

 

Nasan dangina za su nemi su shawo kaina amma ba zan taba amincewa ba, domin irin abinda budurwar ta yi ba abin yafewa bane. Don haka ni babu wani uzuri da za ta bani da zan iya hakura, inji saurayin.

 

 

 

Ya bayyana cewa tun bayan faruwar lamarin ya karbi sakonni daga wajen mata fiye da 100 da suke son ya karbi soyayyar su, sai dai ya ce ya gode musu da nuna damuwar su akan su, amma shi babu wata mace da zai Kara so a rayuwar shi.

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button