Masha Allah, Bidiyon Yadda Wata Mata Ta Haifi Ya’ya Biyar Toffa Kalli Video…

Masha Allah, Bidiyon Yadda Wata Mata Ta Haifi Ya’ya Biyar Toffa Kalli Video…

YADDA AKE WANKAN JANABA DA SIGOGINSA

•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••

 

Da farko dai wankan janaba, ko haila, Haihuwa, juma’a, sallar idi, dukkansu sigarsu iri ɗaya ce, kawai dai suna banbanta ne a niyya.

 

Ita kuma niyyar wanka ana ƙudurta-tane acikin zuciya, kuma niyya tana ƙudurtuwa ne daga daidai lokacin da mutum ya miƙe izuwa ga wankan.

 

Ma’ana: Daga lokacin da mutum ya tashi ga yin wanka to tun daga nan niyyar wanka ta ƙudurtu acikin zuciyarsa.

 

1• Yadda akeyin wankan kuwa shine: Idan mutum ya tanadi ruwansa mai tsarki, a cikin bokiti ne ko baho ko kuma a buta,

 

Idan a bokiti ne ko baho, to abinda zai fara shine zai karkato abin ruwa ya zubo ruwa a hannunsa ya wankeshi sau uku, ko kuma ya ɗebo da wani kofi ya wanke tafukan hannunsa gabansu da bayansu sau uku.

 

Sannan saiya tsoma hannunsa acikin ruwan ya ɗebo ruwa ya wanke ƙazantar dake gabansa, maniyyi ne ko jinin haila ko jinin haihuwa ko waninsa, ya wanke shi da kyau ta yadda bazai ƙara kai hannunsa ga gurin ba.

 

Sannan sai ya wanke hannunsa daya wanke wannan ƙazanta sosai.

 

Sannan kuma sai yayi alwala irin alwalar sallah, idan yazo wajen wanke ƙafa idan yaso saiya bari sai bayan ya gama wanke dukkan jikinsa sannan sai ya wanke ƙafarsa, idan kuma yaso sai ya wanke ƙafarsa gaba ɗayanta nan take, alwala ta kammala.

 

Sannan sai ya ɗebo ruwa kaɗan a hannunsa ya zuba akansa ya murza gashin kansa sau uku.

 

Sannan sai mutum ya zuba ruwa ya fara wanke gaɓoɓinsa na dama sannan kuma na hagu, ma’ana zaka rinƙa bin gaɓɓankana dama kana wankesu daki-daki, idan ka wanke dama saika wanke hagu, harka wanke ko wanne lungu da saƙo na jikinka.

 

Kuma anaso mai wanka ya wanke duk wani lungu najikinsa kamarsu lugun bayan kun-nuwansa da lungun gwiwowinsa da tsakanin mazaunansa da hammatarsa da sauransu.

 

To idan yayi haka shikekan wanka ya kammala tsaf, kuma idan yana so yayi sallah zai iyayin sallah da wannan wanka.

 

2• Idan mai wanka ya tanadi ruwan wankansa mai tsarki, to saiya zubo ruwan a hannunsa ya wanke tafukan hannunsa da bayansu sau uku su fita sosai.

 

Sannan saiya ɗebo ruwa ya wanke ƙazantar gabansa sosai da sosai, ta yadda basai ya ƙara kai hannunsa gurinba idan har yana son yayi sallah da wannan wanka.

 

Sannan sai ya ɗebo ruwa kaɗan a hannunsa ya zuba akansa ya murza sau uku,

 

Sannan sai ya ɗebo ruwa ya zuba a jikinsa gaba ɗaya ya cuccuɗa ko ina da ko ina, basai yabi gaɓoɓin saba, kawai zai zuba ruwane ya wanke dukkan jikinsa lungu da saƙo na jikinsa.

 

Ya kuma tabbatar da ya wanke duk wani lungu na jikinsa har tsakanin mazaunansa.

 

To idan yayi haka to wanka ya kammala, kuma zai iya sallah da wannan wankan idan har bai sake taɓa al’aurarsa ba acikin wankan, idan kuma ya taɓa to ba zaiyi sallah da wannan wankan ba, amma dai wankansa yayi.

 

3• Haka kuma idan mai wanka yaso, idan ya tanadi ruwansa mai tsarki, to zai iya fara wanke jikinsa da soso da sabulu sosai, sannan a daidai lokacin da zai ɗauraye jikinsa da ruwa sai ya ƙudurta niyyar wankan janaba ko waninsa sai ya zuba ruwa ajikinsa ya wanke dukkan jikinsa kuma wankansa yayi.

 

4• Haka kuma idan mai wanka yaje bakin swimming pool ko kogi ko gurin wani ruwa mai tsarki zai iya yin tsalle ya faɗa da niyyar wankan janaba ko waninsa ya wanke dukkan jikinsa tsaf, shima wankansa yayi, idan yana so yayi sallah dashi, sai ya ɗebi ruwa bayan ya fito ya kurkure bakinsa ya kuma shaƙa ya fyace sau uku sai yayi sallarsa.

 

5• Haka kuma idan a ruwan sama ne ko fanfo mai zubo da ruwa daga sama, mutum zai iya shiga cikin ruwan dake zubowa daga sama da niyyar wankan janaba ko waninsa yayi wankansa kuma wankansa yayi.

 

ALLAH shine magi sani.

 

ALLAH kaa gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

 

Duk mai neman ƙarin bayani ya tuntuɓemu ta private.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button