“Sarauniyar Ingila barauniya ce” wani malamin Izala ya bayyana yadda take sace kaya a wajen taro

Sarauniyar Ingila Barauniya Ce” wani malamin Izala ya bayyana yadda marigayiya Elizabeth take sace kayan mutane a duk wajen taron da aka gayyace ta, mutane dadama sunyi mamakin maganar malamin duba da yadda take sarauniya lamba daya a duniya

Malamin yace, matsalar sace-sace jini take bi. “Kalli Sarauniyar Ingila, shiyasa zaka ga duk inda zata je sai antare, tana zuwa wurin nan duk yadda za ayi abinda tafi karfinsa amma sai ta saceshi, saboda matsalar a jinin sune”

Malamin Izalar dai wanda aka ganshi yana wannan bayanin a video a shafin Tiktok yasha maartani sosai daga masu bibiyar shafin, yadda malamin yace Sarauniyar Ingila barauniya ce:

@maryam_revenge #arewa__tiktokers🤣 #arewa__tiktoksers🥰 ♬ original sound – @maryam_revenge

Maganar malamin tajawo mutane dadama sun karyata shi, ga abinda da wasu da suka kalli videon suke cewa:

“Gsky malaman mu basa bincike sai suyita yada tatsuniya”

“Gaskiya ne Aman wanan cuta ne Wanda ake Kira kleptomania ba lalai ne sai sarawniya ba hada nan Nigeria akwai masu irin wanan rashin lafiyan”

“Ba gaskiya bane, Malamai kuna wuce gona da iri wajen bada labari a wajen tafsiri domin burge mabiya”

Kasance da Arewagida.com domin samun labarai irin wadannan. Muna godiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button