Za a sayar da jakar shayin da Sarauniyar Inglila tayi amfani da ita Naira miliyan 6

Wato dai abin mamaki baya karewa a wannan duniya, wani mutum ya sanya Jakar shayin da Sarauniyar Inglila tayi amfani da ita a shekarar 1998 a kasuwa domin sayar da ita akan farashin $12000, Kusan Naira Miliyan 6 kenan a kudin Nigeria.

Mutumin wanda dan kasar America ne (United States) ya sanya jakar shayin Sarauniyar Inglila a kasuwar internet ta Ebay kuma har yana da katin shaida (certificate) daya tabbatar da mallakar jakar shayin wanda Sarauniya Elizabeth tayi amfani da ita kusan shekara 24 da suka gabata. Kalli katin shaidar a kasa:

jakar shayin da Sarauniyar Inglila
Image Credit: Times of India

Za a sayar da jakar shayin da Sarauniyar Inglila

Kamar yadda jaridar Times of India ta rawaito wannan labari, sunce anyi nasarar kwamushe jakar shayin da Sarauniyar Inglila tayi amfani da ita ne a lokacin rayuwarta, yanzu haka kuma tazama makuden kudade har ana shirin sayenta kusan Naira miliyan 6

Karanta Wannan: “Sarauniyar Ingila barauniya ce” wani malamin Izala ya bayyana yadda take sace kaya a wajen taro

Bayan wannan ma, akwai wasu abubuwa da mutane suka mallaka kamar saka hannun sarauniya wanda yanzu haka aka sanya su a kasuwa domin sayarwa a manyan kudade

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button